A bara ne aka sace dalibai da wasu ma’aikatan makarantar su fiye da dari daya, kuma har yanzu akwai ragowar dalibai hannun masu garkuwa da mutane.
Bayan sace daliban makarantar sakandaren Birnin Yauri ranar 17 ga watan yuni na shekara ta 2021, a watan oktoba na shekarar an samu ceto wasu kimanin talatin, sai a watan janairu na wannan shekara 2022 aka ceto wasu talatin.
Bayan wannan adadin da aka ceto da kuma wasu daidaiku da suka samu kubuta, har yanzu akwai ragowar daliban a hannun barayin kuma kusan dukan su ‘yan mata ne, abinda iyayen yaran ke ci gaba da nuna damuwa akan yanayin da suke ciki su da ‘ya'yan nasu.
A hirar shi da Muryar Amurka, wani daga cikin iyayen yace ya dace gwamnati tayi la'akari da cewa ragowar daliban dake hannun barayin ‘yan mata ne wadanda sune ma ya kamata a fara cetowa, amma har yanzu suna cikin jeji tsawon shekara daya.
A lokacin da aka ceto daliban na farko a watan oktoba, gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya karfafa guiwar iyayen akan cewa ba za'a yi Sanya ba wajen ceto dukan daliban.
Amma yanzu wata biyar bayan ceto rukunin daliban na biyu da aka yi a watan janairu wannan shekara, ba'a sake jin komai ba, abinda ke ci gaba daga hankalin iyayen yaran.
Muryar Amurka ta tuntubi mashawarcin gwamnan jihar kebbi a haujin sha'anin tsaro manjo Garba Rabi'u Kamba mai ritaya akan wannan batun yace suna sane da ragowar daliban da ke hannun masu garkuwar dake cikin jeji, kuma suna kan kokarin ceto su, nan bada jimawa ba zasu yiwa jama'a bayanin halin da ake ciki akan lamarin.
Yaran na Makarantar Birnin Yauri dai na daga cikin dalibai mafi dadewa a hannun barayi baya ga na Chibok dake jihar Borno.
Saurari cikakken rahoton Mahmamadu Nasir cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5