Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Ta Sa'o'i 72 Zata Fara Aiki A Yemen

A kasar yamal, manzon musamman na MDD ya bada sanarwan tsagaita wuta na tsawon awa 72 wanda zai fara aiki daga daren Laraba, bayan da ya sami amincewar dukkan bangarorin kasar da ke rigima da junansu.

Ismail Ould Cheikh Ahmed yace tsagaita wannan tashin hanakali zai fara aiki ne da karfe 8 da mintuna 59 na daren gobe Laraba (agogon Yemen) kuma kila za a iya kara lokacin bayan kwanakin ukun farko.

Wannan sanarwa ta biyon bayan kiran da wakilan kasashen Amurka, da Bitaniya da na MDD suka yi ga bangarori masu hannu a rikici yakin basasar kasar na shekaru biyu da su yarda da soma aiwatarda shirin tsagaita wutan da suka ce zasu fara a ‘yan kwanaki nan.