Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Siriya Ta Shiga Rana Ta Biyu

Aleppo, Syria

Da alamar wanzuwar kwanciyar hankali a Siriya, yayin da yarjajjeniyar tsagaita wutar da Amurka da Rasha su ka cimma ke shiga rana ta biyu.

Kwamandan babbar cibiyar mayakan sama ta Amurka, Laftana-Janar Jeffrey Harrigian, ya gaya ma manema labarai a hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon a jiya Talata cewa, Amurka na duba yiwuwar da ita da Rasha su kafa cibiyar hadin gwiwa ta gudanarwa, wadda za ta taimaka wajen dakile aika-aikar ISIS a Siriya.

sai dai kuma Janar Harrigian bai bayyana dalla-dallar inda ake tunanin kafa cibiyar ba, haka kuma bai bayyana irin hadin kan da za a rinka yi ba, ya na mai cewa duk wani dogon bayani a halin yanzu riga-Malam masallaci ne.

Wani baban jami'in gwamnatin Amurka din kuma ya ce, daga yanzu wadanda ya halatta a auna kawai a harin jiragen yaki su ne mayakan kungiyar ISIS da ta al-Nusra.