Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama Ya Shiga Yiwa Clinton Kemfen


Shugaba Obama da Hillary Clinton
Shugaba Obama da Hillary Clinton

Shugaban kasar Amurka Barack Obama a yau Talata yana yiwa tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Hillary Clinton yakin neman zabe yayinda ta dauki yan kwanaki domin ta murmure daga rashin lafiyar pneumonia da ya kamata.

Mr. Obama zai yi magana a wajen Rallyn da za’ayi a Philadelphia sannan zai halarci taron asusun jam’iyyar Democrat.

Clinton ta bayyanawa CNN ranar Litinin zata cigaba da kemfen a karshen wannan satin. Ma’aikatan ta sun bayyana samun kuskuren gane rashin lafiyar wanda ya faru ranar Juma’a, kwana biyu bayan ta bar wajen taro babu shiri a New York, hakan ya jawo cece kuce akan rashin lafiyar ta.

Clinton ta bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa “ Bata yi zaton rashin lafiyar tata zai zama wani babban al’amariba”.

Clinton da abokin karawarta na jam’iyyar republican Donald Trump sun yi alkawarin bayyana takardun da ke dauke da bayanin lafiyarsu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG