Yarjejeniyar Da Aka Kulla Tsakanin Isra’ila Da Hamas Ta Fara Aiki 

Zirin Gaza

Isra'ila ta amince ta ba da damar kai lita 130,000 (galan 34,340) na man fetur a kowace rana a lokacin tsagaita bude wutan, duk da haka wannan adadin kadan ne a kan abin da ake bukata a Gaza, wanda kiyasi ya nuna ana bukatar fiye da litar mai miliyan 1 a duk rana. 

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki hudu da aka cimma tsakanin Isra’ila da Hamas ta fara aiki ranar Juma’a, abin da zai ba da damar fara kai kayayyakin agaji da ake matukar bukata zuwa Gaza da kuma shirin sakin gomman mutane da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su, da kuma Falasdinawan da Isra’ila ke tsare da su.

Ba a dai samu rahoton fada ba sa'o'i bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita wutar. Yarjejeniyar zata kawo sassauci ga al'ummar Gaza miliyan 2.3, wadanda suka sha fama da hare-haren bama-bamai da karancin kayyakin bukata tsawon makonni, da suma iyalai ‘yan Isra'ila da suka damu a kan 'yan uwansu da aka yi garkuwa da su a lokacin harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba, wanda ya janyo yakin.

Musayar farko da za a yi ranar Juma'a za ta kunshi Falasdinawa 39 ciki har da mata 24, har da wasu da aka hukunta a kan laifin yunkurin kisa ko kai hare-hare kan sojojin Isra'ila, da kuma wasu matasa su 15 da aka daure a kan laifuka kamar jifa da duwatsu, a gefe guda kuma a sako 'yan Isra'ila 13 da aka yi garkuwa da su, in ji hukumomin Falasdinu.

Tsagaitawar ta kawo kyakkyawan fatan kawo karshen rikicin a hankali, wanda ya daidaita yankunan Gaza da yawa, ya kuma haifar da tashe-tashen hankula a Yamma da kogin Jordan da aka mamaye, ya kuma haifar da fargabar barkewar rikici a fadin Gabas ta Tsakiya. Ko da yake, Isra'ila ta ce ta kuduri aniyar ci gaba da kai manyan hare-hare da zarar wa’adin yarjejeniyar ya kare.

Isra'ila ta amince ta ba da damar kai lita 130,000 (galan 34,340) na man fetur a kowace rana a lokacin tsagaita bude wutan, duk da haka wannan adadin kadan ne a kan abin da ake bukata a Gaza, wanda kiyasi ya nuna ana bukatar fiye da litar mai miliyan 1 a duk rana.

A mafi yawan makonni bakwai da aka kwashe ana gwabza fadan, Isra'ila ta hana shigar da man fetur zuwa Gaza, tana ikirarin cewa Hamas za ta iya amfani da shi wajen ayyukan soji, ko da yake ta kan bari a shiga da man kadan.

Hukumomin agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun yi watsi da ikirarin, inda suka ce ana sa ido sosai a kan dakon man da ake bukata don kaucewa bala'in yanayin jinkai, tunda ana bukatar man fetur don tada janareto a cibiyoyin tsabtace ruwa, da asibitoci, da kuma sauran muhimman cibiyoyin ababen more rayuwa.

Bangarorin biyu sun amince da sakin mata da yara da farko, a rukunoni daga ranar Juma'a. Isra'ila ta ce yarjejeniyar ta bukaci a tsawaita tsagaita bude wutan da kwana daya don sakin karin mutane 10.

Ma'aikatar shari'a ta Isra'ila ta wallafa sunayen fursunoni 300 da suka cancanci a sake su, galibi matasa da aka tsare a cikin shekarar da ta gabata saboda yin jifa da duwatsu da wasu kananan laifuffuka.