Yarima Harry, Meghan Za Su Ziyarci Najeriya A Watan Mayu

Harry Da Meghan

Yarima Harry da matarsa ​​Meghan za su ziyarci Najeriya a watan Mayu don tattaunawa kan wasannin Invictus, wanda ya kirkira don taimakawa tsoffin sojoji da wadanda ke kan aiki masu raunuka don su samu lafiya, in ji wani jami'in Najeriya a ranar Lahadi.

WASHINGTON, D. C. - Sanarwar da kakakin rundunar tsaron Najeriya Brig. Janar Tukur Gusau ya fitar ba ta bayyana takamaiman lokacin da Yariman zai je nahiyar ta Afirka ba, wurin da ya dade ya ce yana burin ya kai ziyara.

Wasannin Invictus

Amma ana sa ran Harry zai yi wannan balaguron ne bayan wani hidima a Cocin St. Paul na London don bikin cika shekaru 10 na wasannin.

Daga cikin kasashen da suka halarci wasannin na bara har da Najeriya, wadda sojojinta ke yaki da masu ikirarin jihadi a yankin arewa maso gabashin kasar tun a shekara ta 2009.

An dai kwaikwayo wasanin na Invictus ne daga wanda Amurka take yi na “Warrior Games.”

Wasannin Warrior Games

Harry ne ya kafa wasannin na Invictus a cikin 2014 don bai wa tsoffin sojojin da suka ji rauni ƙalubalen fafatawa a wasannin motsa jiki irin na masu bukata ta musamman ko kuma Paralympics.

Harry ya yi aikin soja a Afganistan a matsayin ma'aikacin jirgin sama mai saukar ungulu na Apache a cikin shekarun 2012-2013 kuma ya yi nasara ga tsoffin sojojin da ke buƙatar taimako.

Ziyarar ta sa a Najeriya za ta hada da ayyukan na al'adu kuma "zai karfafa karfin Najeriya a wasannin da kuma yiwuwar daukar nauyin taron a shekaru masu zuwa," in ji Gusau.

AP