Sama da yaran maza 340 ne aka yi garkuwa dasu yayin da wasu ‘yan bindiga da bindigogin AK47 suka kai hari a makarantar sakandaren gwamnati ta yaran maza dake koyar da kimiya a garin Kankara a jihar Katsina a ranar 11 ga watan Disamba.
Yaran sun kwatanta yanda suka yi tafiya a cikin jejin suna shiga gandun daji, suna tsayuwa da rana kana su ci gaba da tafiya a cikin dare babu takalmi suna taka kaya da duwatsu.
Usman Mohammad Rabiu mai shekaru 13 yana cikin yaran da suka dawo gida a ranar Asabar suka hadu da iyalansu.
Ya bada labarin tashin hankali da yace ya saka masa tsoron komawa makaranta.
“A lokacin da suka kwashe mu sun fada mana ilimin book bashi da amfani, inji shi. “Tsoro ya kama ni yayin da suka ce idan sun sake ganin mu a makaranatar book zasu kashe mu.”
Kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram ta Najeriya ta dauki alhakin sace yaran, suna cewa sun kai harin ne saboda suna ganin ilimin book ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.
Iyaye da suke kwalla, sun yi murna da dawowar ‘ya’yan su bayan shiga damuwa sama da mako guda.
“Da naji an sako ‘ya’yan mu na yi matukar farin ciki na ji dadi saboda bana iya bacci, bana iya cin abinci,” inji Murjanatu Rabiu, uwar Habubakar Liti, yaron makaranta da aka sako shi.
Ta kara da cewa “Mun yita kuka saboda ba mu san halin da suke ciki ba. A lokacin da muka gan su sun yi murna sosai koda yake sun dawo gida da rauni a jikin su da kuma yunwa sosai.
‘Yan makarantar sun gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, wanda ya fada musu cewa kada su bari wannan abu ya hana su ci gaba da rayuwa.
An kara samun wasu damuwa bayan sake wani yunkurin sace yaran makaranta a jihar ta Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya a cikin daren ranar Asabar.
‘Yan bindiga sun sace sama da yaran makarantar Islamiya 80 a wani hari, amma jami’an tsaro sun gaggauta kwato yaran bayan wata musayar wuta, a cewar sanarwar ‘yan sanda a ranar Lahadi.
Wannan hari ya tabbatar da matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a arewacin Najeriya.
Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Buhari, Kankara, da jihar Katsina.