Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kubutar Da Dalibai 340 Da 'Yan Bindiga Suka Sace A Katsina


Daliban Da Aka Sace
Daliban Da Aka Sace

Rahotanni daga jihar Katsina na bayyana cewa an ceto yara dalibai 'yan makarantar sakandare da aka sace a Kankara.

Labarai daga majiya mai karfi sun bayyana cewa an sami nasarar kubutar da dalibai 340 da aka sace su a makarantar sakandaren kwana da ke garin Kankara ta jihar Katsina a ranar Juma'a da ta gabata.

Rahotannin sun bayyana cewa an sami nasarar kwato wadannan daliban ne a wani yankin jihar Zamfara. Gwamnatin jihar ta Katsina ta tabbatar da cewa yanzu haka wadannan daliban suna hannun karkashin kulawar ta kuma suna cikin koshin lafiya.

Daliban Da Aka Sace
Daliban Da Aka Sace

Nan ba da jimawa ba ake sa ran gwamnan jihar ta Katsina Alh. Aminu Bello Masari zai karbi wadannan daliban da kuma bayyana wa duniya halin da suke ciki.

Ga rahoton da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya hada muna cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00

Daliban Sakandaren Kankara: Yadda Aka Yi Na Kubuta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, da jihar Katsina.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG