Hakan kuma na faruwa ne saboda rashin ababan da za su saukaka musu gudanar da rayuwarsu cikin sauki a makarantun, a cewar gamayyar kungiyoyin nakasassu da ake kira JONAWD a takaice.
A kasashe masu tasowa musamman a nahiyar Afrika ba kasafai ake maida hankali kan bukatun masu nakasa ba, watakila kom saboda halin ko in kula da hukumomi ke nunawa ko kuma ana karkata kudaden da aka ware domin hakan.
Ire-ire wadannan kalubale kuma na haifar da cikas ga yadda musamman yara nakasassu ke gudanar da rayuwarsu a fannonin daban daban kamar a makarantu.
Dalilin haka Jummai Ali ta tattauna da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin nakasassu a Najeriya, Dr Samuel Ankeli, inda ta fara da tambayar shi, dalilan da ya sa adadin yaran nakasassu da ba sa zuwa makarnata ya kai har miliyan uku:
Your browser doesn’t support HTML5