Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karancin Abinci Ya Yi Kamari A Yankin Da Boko Haram Ta Daidaita


'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.
'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.

Jami’an aikin jinkai sun yi gargadi yau Jumma’a cewa, karancin abinci ya yi Kamari ainun a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da yaki ya daidaita, kuma yankin yana iya fuskantar matsalar karancin abinci.

Majalisar Dinkin Duniya tayi kiyasin cewa, kimanin mutane miliyan hudu da dubu dari hudu ne a Arewa maso Gabashin Najeriya suke fama da matsanancin karancin abinci sakamakon yakin da da ake yi tsakanin kungiyar Boko Haram da kuma rundunar sojin kasar da na makwabtanta.


Yana yiwuwa sassan yankin da suke da hadarin shiga, ko kuma aka katsesu daga sauran ciboyoyin agaji suna fuskantar karancin abinci, bisa ga rahoton cibiyar tada tsimin jama’a kan yiwuwar fuskantar yunwa.


Darektar cibiyar na wucin gadi a Najeriya Sory Quane yace” idan bamu dauki mataki ba, matsalar zata zama bala’i."


Wani jami’in hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ya bayyana cewa, galibin wadanda suke fama da cutar rashin abinci mai gina jiki, mutane ne da suka isa sansannoni daga wuraren da basu samun abinci.

XS
SM
MD
LG