Yara A Arewacin Habasha Na Cikin Tsananin Bukatar Kariya Da Taimako

“Matsainacin halin take hakkin yara da ake yi a duk fadin Tigray bai nuna alamar raguwa ba, kusan watanni bakwai ke nan tun lokacin da fada ya barke a arewacin Habasha.

“Fiye da yara 6,000 ba tare da rakiya ko kuma wadanda suka rabu da iyayansu ba an gano su ya zuwa yanzu, kuma an yi musu rajista don kariya da taimako.

Muna tsoron akwai karin yara da yawa da ke buƙatar tallafi a yankunan da ba za mu iya kaiwa ba saboda rashin tsaro ko ƙuntatawa hanyoyin shiga da ɓangarorin rikicin suka sanya.

Bin dindigen iyalai ya yi wuya ta hanyar karancin sadarwa, karancin kasancewar ma'aikatan sa kai, da karancin hanya layukan sadarwa. “Har yanzu mata da ’yan mata na fuskantar mummunan halin lalata.

Fiye da mutane 540 da suka tsira sun sami taimako ta hanyar shirye-shiryen UNICEF tun bayan barkewar fada a watan Nuwamba na 2020, amma tsoron ramukan gayya, ya hana samun adadin lambobin da ba za su iya samun kulawa da aiyukan da suke bukata cikin gaggawa ba.

“Yara, iyaye da masu kulawa suna ba da rahoton tsananin damuwa da takaici, cewar suna tsoron ramuwar gayya ko hari. Matasa maza sun yi ta magana game da tsoron daukar su a matsayin ma'aikata ga bangarorin da ke rikicin. Abokan hadin gwiwar UNICEF na ci gaba da bayar da rahoto game da kame-kame da tsarewa ba bisa ka'ida ba.