Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

G7 Kan Rikicin Tigray A Ethopia


The White House
The White House

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, tare da Ministocin Harkokin Waje na G7 da suka hada da Canada, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, Birtaniya da Babban Wakilin Tarayyar Turai suna matukar damuwa game da rahotannin na kwanan nan kan take hakkin bil adama da cin zarafinsu da keta dokar jinkai na ƙasa da ƙasa a lardin Tigray na Habasha.

Fada ya fara ne a watan Nuwamba lokacin da Firayim Ministan Habasha Abiy Ahmed ya tura sojojin tarayya zuwa cikin Tigray da nufin "dawo da doka" ta hanyar fatattakar kungiyar 'Yanci ta Tigray People’s Liberation Front bayan wani hari da aka kai wa sansanin sojojin tarayya. Tun lokacin da fadan ya barke, mutane da yawa suka gudu daga Tigray suka nemi mafaka a makwabciyar Sudan.

Kungiyar ta G7, a cikin wata sanarwa, “ta yi Allah wadai da kisan fararen hula, lalata, cin zarafin jinsi da nuna bambanci, da harbe-harbe da tilasta gudun hijira ga mazaunan Tigray da Eritrea. Wajibi ne dukkan bangarorin su kame kansu, su tabbatar da kare fararen hula da mutunta 'yancin bil adama da dokokin ƙasa da ƙasa. "

Amurka da kawayenta suna fatan gwamnatin Habasha za ta aiwatar da kudurinta na hukunta wadanda ke da alhakin irin wannan cin zarafin.

Kwamitin Kare Hakkin bil-Adam na Habasha da Ofishin Babban Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya na Kare Hakkin bil-Adam sun amince da gudanar da binciken hadin gwiwa kan take hakkin bil adama da duk bangarorin suka yi a rikicin na Tigray. Yana da mahimmanci a aiwatar da bincike mai zaman kansa, a bayyane, kuma ba tare da nuna son kai a cikin laifuffukan da aka ruwaito kuma wadanda ke da alhakin wannan take hakkin bil adam a hukunta su ba.

Amurka da kawayenta na G7 "sun bukaci bangarorin da ke rikicin su hanzarta, ba da damar kai kayan agaji ba tare da wata matsala ba." Akwai damuwa matuka game da tabarbarewar karancin abinci, tare da yanayin gaggawa da ake ciki a duk yankuna masu yawa a tsakiyar da gabashin Tigray.

Firayim Ministan Habasha Abiy a kwanan nan ya ba da sanarwar cewa sojojin Eritrea za su janye daga Tigray. Amurka da kawayenta sun yi kira da cewa wannan tsari ya kasance "da sauri, ba tare da wani sharadi ba, kuma za a iya tabbatar da shi."

Sanarwar hadin gwiwar ta ci gaba da kiran " a kawo karshen tashin hankali da kafa kyakkyawan tsarin siyasa, wanda dukkan 'yan Habasha za su amince da shi, gami da wadanda ke yankin na Tigray, kuma hakan zai haifar da ingantaccen zabe da kuma sasantawa tsakanin kasa."

"Mu mambobin G7 a shirye muke don tallafawa ayyukan jinkai da bincike kan take hakkin bil adam."

XS
SM
MD
LG