‘Yar Tseren Gudu Daga Nijar Ta zo Ta Hudu A Tseren mita 200 A Gasar Tseren Gudu Na Duniya
Zamu soma labarun wassanin mu na ranar yau da jamhuriyar Nijar, inda 'yar kasar mai suna Amina Seyni da ke halartar tseren gudu na duniya a Eugene, Jihar Oregon ta kasar America, ta ta zo ta 4 a tseren mita 200 a karshen makon da ya gabata.
Gabanin haka, shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijer ne da kansa, Bazum Mohamed, ya kira ‘yar tseren domin kara mata kuzari da tokararta domin ta kara jin kwarin gwiwa kamar yanda zaku ji.
“Amina kina lafiya? inji shugaban kasar, ina fatan zamu ji labari mai dadi a karshen wannan sukuwar taki?
Amina Seyni ta amsa da cewa" Insha Allahu shugaban kasa".
Wannan dai, shine karo na farko da Amina Seyni da ke rike da kambun tseren mita 200 na nahiyar Afrika, ta samu shiga tseren na duniya, kuma matsayi na 4 da ta samu bayan ‘yan Jamaica 2 da ke rike da kambun duniya na 1 da na 2 cewa Sherika Jackson da Shelly-Ann sai ta 3 ita ce ‘yar Burtaniya Dina ASHER-SMITH yayin da Amina Seyni ta jamhuriyar Nijer ta tamo ta 4.
A yau ne a wassanin kwallon kafa na Nahiyar Turai dake wakana yanzu haka a kasar Ingila, a ke can ana karawa a wasan kusa da na karshe tsakanin Mai masaukin baki cewa Burtaniya da kasar Sweden, yayin da a gobe idan Allahu ya kai mu, za a sake karawa a wasan kusa da na karshe na 2 tsakanin kasar Faransa da kasar Jamus.
A yau ne kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus ta bada sanarwar sayen matashin nan dan kasar Faransa dake buga wa club din RENNES, wanda zai buga mata kawallo har tsawon shekaru 5 a nan gaba, cewa da Mathys Tel, matashi Dan shekaru 17 a duniya da ya buga wasanni 10 na ligue one ta kasar Faransa a kakar wasannin da ta gabata, yayin da ya kasance zakaran Turai tare da kasar Faransa na 'yan wasa 'yan kasa da shekaru 17 na nahiyar Turai a Bana.
Club din na Bayern Munich ya kashe tsabar kudi har yuro miliyon 28 da jikka 500, kwatankwacin sefa Biliyon 18 da miliyon 659 da jikka 235.
Yau Talata ne, kunyiyoyin kwallon kafa na kasar Burtaniya suka zabi Alison Brittain yar shekaru 57 da haihuwa a matsayin shugabar hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila.
Ita dai Alison Brittain, ta gaji Gary Hoffman da guguwar sayar da kungiyar kwallon kafa ta NewCastle ga masu jari 'yan kasar Saudi Arabiya ta rutsa da shi a watan Nuwamban da ya gabata.
I zuwa yanzu dai, Peter McCormick ne ke rike da rikon kwaryar kungiyar kwallon kafar ta kasar Burtaniya.
Saurari cikkaken bayani a rahoton Harouna Mammane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5