'Yar Gudun Hijira Daga Maiduguri Zuwa Gombe Da 'Ya'yanta

Wata mata da 'ya'yanta biyu a dab da tashar motar titin Jos a Maiduguri tana jiran shiga mota.

Wata matar da ta tsere da 'ya'yanta daga Maiduguri ta bayyana irin ukubar yunwa da wahalar da suka sha a hanya kafin su kai Gombe
Matsalar yunwar da aka shiga, da kuma yanayin rashin kwanciyar hankali, sune manyan dalilan da suka sanya wata mace tare da 'ya'yanta tserewa daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, zuwa Gombe, a bayan da aka kafa dokar-ta-baci a jihar, aka kuma kafa wata dokar ta hana fita a wasu sassan babban birnin.

Wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad, ya ci karo da wannan mata da 'ya'yanta a garin gombe, inda ta ce sun yini a bakin kofa ranar jumma'a su na neman hanyar fita daga garin Maiduguri, amma sojoji suka hana su.

Matar ta yi bayanin yadda aka rika kokawar sayen burodi a saboda tsananin yunwa da rashin hanyar samun abinci a lokacin da suke jiran sojoji su ba su iznin shigewa zuwa inda suka dosa.

Ga cikakken bayanin da matar ta gabatar a kasa:

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Matar Da ta Gudu Zuwa Gombe Daga Maiduguri Da 'Ya'yanta - 1:54