Kawo yanzu su 'yansandan kwantar da tarzoma wato Mobile ko kuma mobilawa, sun wuce inda sojoji suka ja daga har sun kai Kasuwar Dare wurin da sojoji basu iya zuwa ba.
Shaidu na ganin da ma 'yansandan kwantar da tarzoman aka ba aikin da 'yan Boko Haram basu cafke garin ba.
Malam Ahmed Sajoh dan asalin garin na Mubi ya bayyana abun da suke bukata. Yace da so samu ne sai a yiwa garin kawanya a fitar da 'yan Boko Haram a maida masu garinsu. Rokonsu ke nan.
Wani masanin harkokin tsaro Dr Abdullahi Bawa Wase yace akwai irin rawar da 'yansandan kwantar da tarzoma zasu iya takawa. Yace a kowace kasa idan irin hakan ya faru ana kwasar 'yansandan kwantar da tarzoma a hadasu da sojoji domin a shawo kan lamarin. Mobilawa sukan taka rawar da take da tasiri a kwantar da tarzoma irin ta 'yan Boko Haram.
A yakin basasan Najeriya tun daga farko an yi irin wannan buguzumzum lokacin da sojoji suka fara ja da baya suna bayar da wasu hujjojin banza. A wannan zamanin ma 'yansanda suka nuna karfin hali suka jajirce daga nan sojoji suka ga zasu ji kunya kana suka biyo baya. An kuma samu nasara.
Har yanzu dai su 'yan Boko Haram na cigaba da tsara nasu irin shari'ar inda suka fara aurar da wasu 'yan mata da matan da mazajensu suka gudu kamar yadda shaidu suka tabbatar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5