Yankin Sahel Na Bukatar Taimako Don Yaki Da Masu Tsattsauran Ra'ayi - Majalisar Dinkin Duniya 

United Nations Human Rights Council

Yankin Sahel na Afirka ya zama wurin da ake fama da mummunan tashin hankali, amma rundunar hadin gwiwa da aka kafa a shekarar 2014 domin yakar kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar IS da al-Qaida da sauran su, ta kasa dakile kutsen da suke yi. 

WASHINGTON, D.C. - Wata babbar jami'iar Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Talata cewa, in har ba a samu kwakkwaran goyon bayan kasa da kasa da hadin gwiwar yanki ba, rashin zaman lafiya zai fadada zuwa kasashen Yammacin Afirka.

Kayan aikin soji da gwamnatin Amurka ta ba Jamhuriyar Nijar gudummuwa

Mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya a Afirka, Martha Pobee, ta shaida a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, "ci gaba da cimma matsaya kan yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da aikata laifuka a yankin Sahel na matukar bukatar nazari.

Rundunar yaki da ta'addanci wadda a yanzu ta kunshi kasashen Burkina Faso, Chadi, Mauritania da Nijar, sun yi rashin Mali shekara guda da ta wuce lokacin da gwamnatin da ke mulkin kasar ta yanke shawarar ficewa daga rundunar.

Pobee ta ce haka kuma rundunar ba ta gudanar da wani gagarumin aikin soji ba tun watan Janairu.

Ta kara da cewa, rundunar tana daidaitawa da sabbin abubuwa: Faransa tana tura dakarunta na yaki da ta'addanci daga Mali zuwa Nijar saboda takun-saka da gwamnatin mulkin soji da kuma matakin da Mali ta dauka na barin sojojin hayar Rasha na Wagner zuwa yankinta.

A cewarta, a baya-bayan nan Burkina Faso da Nijar sun karfafa hadin gwiwar soji da kasar Mali domin dakile karuwar hare-haren masu tsattsauran ra'ayi, amma duk da wannan kokarin, rashin tsaro a yankin na kan iyaka yana ci gaba da karuwa.

Sojojin Tafkin Chadi-Nijar

Pobee ta soki kasashen duniya, tana mai cewa rashin daidaito tsakanin masu hannu da shuni da abokan hulda, ya bar rundunar ta hadin gwiwa ba tare da isassun kudade ba da sauran tallafin da ake bukata don samun cikakken aiki da cin gashin kai ta yadda za ta iya samun “ikon taimakawa wajen samun zaman lafiya a yankin Sahel.”

Ta kara da cewa, a watan Yuni ne ake sa ran za a kawo karshen yarjejeniya tsakanin Majalisar Dinkin Duniya, EU da rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalisar a kasar Mali, ta samar da man fetur, abinci, magunguna da kuma aikin injiniya ga rundunar ta hadin gwiwa a watan Yuni, tare da bayyana fatan kwamitin sulhun zai yi la'akkari da haka don ba da tallafin kudi don ayyukan samar da zaman lafiya a Afirka.

-AP