Ana iya cewar duniya na kara dunkulewa waje daya, a yadda masana ke gani. Idan aka yi la’akari da yadda kimiyya da fasaha ke dauke da kusan komai na rayuwar yau da kullum.
Masana na kara bayyanar da fargabarsu dangane da yadda komai ke zamowa cikin daki daya, a wannan karni na 21 da ake ciki, ana iya ganin sabon tsarin G5, wanda ke kara karfin yanar gizo a fadin duniya, a matsayin barazana ga bayanan sirri na mutane.
Sabon tsarin na G5 yana da karfin yanar gizo da mutane za su iya amfani da shi, wajen aika sako komi girmansa da ya shafi bidiyo, ko wasu takardu masu nauyi cikin kankanin lokaci.
Ku Duba Wannan Ma Facebook Ya Kirkiri Manhaja Mai Bayyanar Da Hotunan BatsaHaka tsarin zai ba na’urori damar kai sako ga wasu sassa daban-daban a fadin duniya.
Idan aka duba yadda gidajen jama’a ke zagaye da nau’rori da ke dauke da bayanan mutane, kamar a gida akan iya samun na’urar dumama daki, kararrawar baki ta gida, wayoyin hannu da dai sauransu.
Haka akan titi na’urar ba da hannu na amfani da yanar gizo, kyamarorin kan hanya, motoci, akasarin wadannan na'urorin suna aiki ne tare da yanar gizoba mai karfin G5 musamman a kasashe masu tasowa.
Masanan na ganin cewar wannan babbar barazanace ga rayuwar yau da kullum, domin kuwa duk wani abu da mutun ka iya yi ana iya ganin shi a duk lokacin da wadannan kamfanonin suka so hakan.
A cewar Mr. Cody Brocious, mai nazari a wani kamfani na HackerOne, hakan zai iya ba ‘yan kutse damar shiga cikin bayanan mutane don satar bayanan su da kuma amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.