Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Ya Kirkiri Manhaja Mai Bayyanar Da Hotunan Batsa


A jiya Laraba ne kamfanin Facebook ya sanar da cewar a cikin rabin wannan shekarar ya cire hotuna na yara masu dauke da al’aurar yaran fiye da milliyan 8.7, wanda kamfanin yake amfani da wasu sababbin manhajoji da zasu iya gano duk wani hoto da aka saka a shafin dake dauke da tsiraicin yara.

Sabuwar manhajar tayi aiki cikin shekara daya da ta iya ganowa da kuma cire duk wasu hotuna da suke nuna al’aurar mutane maza ko mata, da kuma hotunan yara kanana. Hakan zai kara karfafawa kamfanin yaki da daura hotunan da basu kamataba a kan shafin.

Haka kuma manhajar zata taimaka wajen gano wasu mutane da kanyi amfani da shafin, wajen yada ko kuma aiwatar da ayyukan ashha, kamar maganganun batsa, neman hanyar saduwa don aikata shashabci da cin zarafin yara da mata.

Shugabar sashen kula da duniya ta kamfanin na Facebook Antigone Davis ce ta bayyana ma kamfanin dillanci labarai na Reuters hakan a wata ganawa, ta kuma kara da cewar sabon tsarin zai taimaka musu wajen cinma burinsu da gaggawa, da kuma kawo karshen yadda ake amfani da shafin ta hanyoyi da basu dace ba.

Kamfanin kuma a shirye yake ya kawo karshen yadda ake amfani da kafofin yanar gizo don cin zarafi, da fadan kausasan maganganu ga juba, wanda hakan ya sabama ainihin makasudin kirkirar shafin na sada zumunci cikin sauki.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG