Jabir Mustapha Sambo, matashi da ke gudanar da karatunsa a kasar Birtaniya, a matakin digiri na biyu ya ce babu wata hanya da ta kamata ace matasa sun ba da karfin su da ya ta wuce wajen neman ilimi don ciyar da kasa gaba.
A iya bincike da yake gudanarwa, yana ganin fannoni biyu da suke rike da duniya su ne ilimin huldar kasashe a duniya, wato diflomaciyya da kuma aikin jarida.
A cewar shi, wadannan fannoni biyu suna taka muhimiyyar rawa wajen ilmantar da jama'a da ba su duk wata dama da suke bukata don samun romon dimokaradiyya.
Babban abin da ya kamata matasa su maida hankalinsu akai shi ne, neman ilimi a duk matakai, ba tare da wani shamaki akan fannin da mutun zai karanta ba don tunanin ta nan ne kawai zai iya samun kudi, yana mai cewa tunanin mutum ya kamata ya koma kan yadda zai ba da tashi gudunmawar wajen ganin al'ummah ta ci gaba.
Facebook Forum