'Yan Yankin Niger Delta Na Nuna Shakku Kan Lafiyar Buhari

  • Ibrahim Garba

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Bisa ga dukkan alamu 'yan Najeriya musamman na Niger Delta suna ci gaba da kasancewa cikin rudani dangane da lafiyar Shugaban kasa Muhammad Buhari.

Wasu na gani shugaban ya na fama da wata rashin lafiya ce da har yanzu ba'a bayyanawa al'ummar kasar ba.

Wannan lamarin na rashin sanin tabbas ya haifar da ka-ce-na-ce musamman a kudancin kasar inda koda yaushe suna batun kabilanci da nuna banbanci wajen bayyana halin da kasar ke ciki.

Wani mai suna Daniel ya ce da ya ji an ce shugaban ba shi da lafiya daga baya kuma aka ce ya rasu.

Ya ce su a Niger Delta suna ganin shugaban ya mutu idan kuma ba zai dawo Najeriya ba to yakamata a yi cikakken bayani domin kasar ta sani.

Amma wani Riki Wike ya ce suna addu'a shugaban ya dawo lafiya ya ci gaba da aikinsa amma dai "akwai shakku da yawa a zukatanmu", inji shi.

Shi Umar Riskuwa cewa ya yi 'yan Najeriya nada hakkin su san me shugabansu ya ke ciki, ya na mai cewa abu ne wanda ya kamata a yi bayaninsa - bayani kuma na tsakani da Allah.

Mukarraban shugaban sun hakikance ya na nan lafiya tare da cewa kowane lokaci daga yanzu ya na iya dawowa kasar.

Da yammacin jiya Alhamis, hukummin kasar suka fitar da wasu sabbin hotuna dake nuna shugaba Buhari da wasu mukarraban jam'iyarsa a lokacin da suka kai mai ziyara a London.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Yankin Niger Delta Na Nuna Shakku Kan Lafiyar Buhari - 3' 33"