Shugaban Ghana John Dramani Mahama na jami’iyar National Democratic Congress mai mulki da dan takarar babban jami’iyar adawa ta New Patriotic Party Nana Addo Dankwa Akufo-Addo da wasu yan takarar shugaban kasar sun karbi takardun shiga takara daga hukumar zaben kasar don shiga zabe ranar 7 ga watan Disamba. Masu takarar zuwa majalisa suma sun fara karbar takardunsu na shiga takara.
WASHINGTON, DC —
Masu takarar shugaban kasar zasu biya Dala Dubu 12 da dari biyar da biyar, a yayinda da ‘yan takarar majalisar zasu biya Dala Dubu 2,500 a matsayin kudin tsayawa takara, banda cika wadansu sharudda da hukumar zaben ta gindaya.
Ranakun 29 da 30 ga wannan watan Satumba hukumar zaben ta ware a hukumance da zata amshi takardun masu shiga takarar da suke sha’awar tsayawa zabe a watan Desimba inji kakakin hukumar Eric Dzakpasu.
An zargi hukumar zabe da jam’iyar NDC mai mulki da yiwa ‘yan takara zagon kasa a yunkurinsu na maida takardunsu na tsayawa takara a babban zaben da aka gudanar a shekarar Nana Konadu Agyemang Rawlings tace an gurguntar da niyarta ta wakiltar jam’iyarta ta NDP a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2012.