'Yan Takarar Jam’iyar Republican Sun Fafata A Muhawarar Farko Ta Neman Tikitin Shugaban Kasa Na 2024

Muhawarar 'Yan takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Republican

'Yan takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Republican sun fara muhawara a daren Laraba a babban taron farko na zaben Shugaban kasa na shekara mai zuwa.

Sai dai tsohon shugaban kasar Donald Trump bai shiga muhawarar ba bisa hujjar cewa, ya yi wa sauran masu kalubalantarsa fintinkau ta yadda ba ya bukatar yin muhawara dasu.


'Yan takara tara sun cancanci yin muhawarar da ake gudanarwa a Dandalin Fiserv a tsakiyar yammacin birnin Milwaukee da ke jihar Wisconsin. Amma Trump, wanda ke kan gaba a tsakanin masu jefa kuri'a na jam'iyyar Republican a duk fadin kasar don zaben fitar da gwani na jam'iyyar a 2024, ya yanke shawarar cewa ba shi da wani abin da zai samu a fafatawar sa'o'i biyu da sauran 'yan Republican din.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump

An tuhumi Trump da aikata wasu laifuka hudu da suka hada da tuhume-tuhume 91 na laifuka da ya aikata kafin, a lokacin shugabancinsa, da kuma bayan shugabancin sa, wadanda suka kare a farkon shekarar 2021.

Ya ce zai mika wuya domin kama shi a jihar Georgia, ranar Alhamis, dangane da tuhuma ta hudu, da ake zargin sa da yin zagon kasa da kuma yin katsalandan a yunkurin sake cin zaben 2020 da ya gaza yin nasara a kudancin jihar.

Amma ko a hakan, yana kan gaba da kusan kashi 40 cikin 100 a kan abokin hamayyarsa na Jam'iyyar Republican, Gwamnan Florida Ron DeSantis, tare da sauran 'yan adawar Republican da su ka samu kasa da kashi 10% kowannensu a zaben kasa.

Gwamnan jihar Florida Ron DeSantis

Duk da rashin Trump, masu sauraron talabijin don kalon muhawara a tashoshin Fox News na iya raguwa da miliyoyin masu jefa kuri'a.

Amma shugaban jam'iyyar Democrat Joe Biden, wanda ke neman sake tsayawa takara kuma da alama zai fuskanci Trump ko kuma daya daga cikin sauran 'yan jam'iyyar Republican a zaben watan Nuwamba na 2024, ya shaida wa manema labarai cewa, "Zan yi kokarin gani - iya gwargwadon da zan iya yi. ”

Duk da haka, muhawarar ba za ta yi tasiri sosai ga Trump ba – zai cigaba da kasancewa kan gaba ba tare da la’akari da abin da ya faru ba.