'Yan takara dake neman shugabancin Amurka zasu fafata yau a jihohi biyar

'Yan takaran bangaren Democrats Sanders da Clinton

A cigaba da zaben fidda gwani daga jam'iyyun Democrats da Republican saboda zaben shugaban kasa yau Talata zasu fafata a jihohi biyar da suke da mahimmanci

A yau Talata, an bude rumfunan zabe a jihohi biyar, inda masu kada kuri'a zasu bayyana zabinsu tsakanin masu takarar shugabancin Amurka, inda Donald Trump a banagren Republican, da Madam Hillary Clinton na Democrats wadanda suke kan gaba ahalin yanzu suke kokarin kara tazara tsakaninsu da sauran abokan takara, su kuma sauran suke kokarin samun karin goyon baya domin su ci gaba da fafatawa.

Jihar Florida tana da muhimmanci a zaben na yau, inda wanda ya sami nasara a banagaren 'yan Republican zai kwashe wakilai 99 baki daya. Sabbin kuri'ar neman jin inda ra'ayoyin 'yan jihar suka karkata, sun nuna Donald Trump, yake kan gaba da maki 17 cikin dari da dan takara mafi kusa da shi, watau senata Marco Rubio, wanda yake da matukar ya sami nasara domin karfafa ci gaba da takara da yake yi.

Wata jiha da take da tasiri a zaben na yau, itace jihar Ohio,inda Trump suke karo da Gwanan jihar kuma dan takarar shugaban kasa John Kasich. Mitt Romney,wanda shine dan takarar shugaban kass na jam'iyyar Republican a shekara ta 2012, da shugaba Obama ya kayar, yayi yakin neman zabe tared a Gwamna Kasich a Ohio, a yunkurin takawa Trump birki, na samun nasara wakilai 66 daga jihar.

A jihar Carolina ta arewa, da Missouri, da Illinois, tazarar da Trump yake da ita kan senata Ted Cruz na jihar Texas, bata da yawa.

'Yan takaran bagaren Republican. Daga hagu Rubio, Trump, Cruz, da Kasich