Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Lallai Jam'iyyar Republican Ta Amurka Ta Yi Gangaminta Na Watan Yuli Ba - Inji Shugabanta


'Yan Takarar Shugabancin Amurka a Wajen Mukabala. Daga Hagu Zuwa Dama: Marco Rubio, Donald Trump, Ted Cruz, John Kasick.
'Yan Takarar Shugabancin Amurka a Wajen Mukabala. Daga Hagu Zuwa Dama: Marco Rubio, Donald Trump, Ted Cruz, John Kasick.

‘Yan takarar neman shugabancin Amurka a jam’iyyar Republican da ke ta hantarar juna suna nan suna shirin shiga zaben fidda gwanin da za a ayi ranar Asabar din nan a wasu jihohi da dama.

Shugaban jam’iyyar ta Republican da ke fama da rarrabewar kan membobinta, yace ba lallai bane su yi gangamin zaben fidda gwani ba a watan Yuli mai zuwa kamar yadda suka saba ba.

Reince Priebus yace, ‘yiwuwar yin gangamin jam’iyyar mu kalilan ne”. Ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron siyasa na shekara-shekara da aka yi a jihar Maryland da ke makwabtaka da birnin Washington ta nan gundumar Columbia.

Shugaban yace, ko wa aka zaba a watan Yulin mai zuwa to zasu taru su goya masa baya 100 bisa 100 ba tare da kiki kaka ba. Reince, ya jaddada cewa ba maganar son kai ga wani dan takarar jam’iyyarsu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG