Baya ga kisan Kutemeshin, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa an kara kashe mutane 23 a kananan hukumomi biyar da ke fadin jihar, ciki har da Karamar Hukumar Birnin Gwari. Wani Dan yankin Saulawan Karamar hukumar Birnin Gwarin da ke gudun hijira yanzu haka, ya ce garuruwa da dama yanzu sun zama Kufayi saboda fargabar hare-haren 'yan bindiga.
Sabuwar sanarwar da kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya fitar da yammacin jiya Talata dai ta ce jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a kananan hukumomin Giwa, Chukun, Kachia, Igabi da Birnin Gwari.
Dama dai Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya sha alwashin fito-na-fito da 'yan bindiga a matsayin mafita game da da matsalar tsaro.
Yanzu dai kusan kullun sai ofishin Kwamishinan tsaro na jihar Kaduna ya fitar da sanarwar harin 'yan bindiga a daya ko wasu daga cikin yankunan cikin kananan hukumomin Giwa, Chukun, Kachia, Igabi, Birnin Gwari ko kuma Kajuru. Amma dai gwamnatin ta kan sanar da Kokarin da jami'an tsaro ke yi don kawo karshen matsalar tsaro a fadin jihar baki daya.
A saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5