‘Yan Siyasa A Najeriya Sun Soma Daukar Alkawuran Bin Doka Yayin Da Za A Fara Yakin Neman Zabe

Wasu ‘Yan Siyasa A Najeriya 

A yau Laraba 28 ga watan Satumba aka fara yakin neman zaben 2023 a hukumance a Najeriya.

SOKOTO, NIGERIA - Sai dai wasu masana na ganin alkawuran kura ne ‘yan siyasa ke dauka domin ba cika su za su yi ba.

A wasu kasashen duniya hada-hadar lamuran siyasa wasu lokuta sukan zo da tashe-tashen hankula, musamman tsakanin magoya bayan jam'iyun da ke adawa da juna, kamar yadda ya sha faruwa a Najeriya.

Hakan baya rasa nasaba da yadda wasu kungiyoyi ke shiga tsakani ta hangar kulla yarjejeniya tsakanin jam'iyu tun kafin lokacin zabe, akan su gudanar da lamura cikin lumana.

APC, PDP

Wannan karon rundunar 'yan sandan Najeriya ce ta shiga sahun gaba wajen hada ‘yan siyasa wuri daya, don su yi alkawari akan bin doka ga yekuwar neman zabubukan da zasu gudanar.

Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Sakkwato Muhammad Usaini Gumel ya ce sun hada ‘yan siyasan ne domin su aza su ga hanya.

Ya kuma ce sun kira su ne suka sanar da su tsarin dokokin yekuwar neman zabe don su kiyaye, kuma sun aminta har sun bayar da alkawari a rubuce cewa zasu bi doka.

Alkawura da ‘yan siyasa suka dauka sun hada da bin tsarin doka a yekuwar da zasu yi, zasu hada kai da hukumar zabe wajen tsari jadawalin fita yekuwa, don kaucewa haduwar jam'iyun adawa a hanya daya lokacin yekuwar, da kuma ba za'a yi amfani da jami'an tsaro wadanda doka bata aminta dasu ba.

Wakilan jam'iyun siyasa da suka shedi taron kulla daukar alkawarin sun ce sun aminta da tsarin kuma sun yarda zasu yi aikin da alkawarin da suka dauka.

Tinubu, hagu, Atiku dama (Hoto: Facebook: Kashim Shettima/Atiku Abubakar

Masana lamurran kimiyar siyasa da wannan da zaman lafiya na ganin wadannan alkawura suna wuyar cikawa domin ba yau aka soma irinsu ba, kamar yadda farfesa Tanko Yahaya Baba na jami'ar Usmanu Danfodiyo ke gani.

Ya ce cika alkawuran yana da wuya saboda ko an karya su ba wanda za'a hukunta, kuma su kansu ‘yan siyasa ke karya irin wadannan alkawulla.

Ya ce muddin ba an rika hukumta masu kawo tashe-tashen hankula da masu daure musu gindi ba, ba za'a taba samun zabe mai tsabta ba, wanda ba tashin hankali.

Masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro da bin doka suna jaddada kiraye kiraye akan gudanar da lamurran yekuwar neman zabe da ma zabubukan cikin lumana, sai dai yanzu lokaci ne kadai zai nuna ko wadannan alkawura zasu samu cika ko akasin haka.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Siyasa A Najeriya Sun Soma Daukar Alkawuran Bin Doka Gabanin Zabe .mp3