Da yake jawabi a albarkacin wannan rana shugaban ‘yan Shi’a na kasa Sheik Salissou Ahmed Lazaret ya gargadi shugabanin duniya akan kwatanta adalci a tsakanin jama’a domin, a cewarsa, rashin yin hakan na kan gaba a jerin dalilan rigingimun da ake fama da su a kasashe da dama.
Jigo a kungiyar fafutika ta Sauvons le Niger Salissou Amadou da ke bayyana ra’ayinsa na cewa wajibi ne al’umma tallakawa su dawo kan hanyar gaskiya.
Karancin adalci a sha’anin shari’a kokuma rashinsa kwata kwata a galibin kasashen duniya, shine mafarin halin da ake ciki a yau, saboda haka wajibi ne a dauki matakai kan halin da fannin ke ciki muddin ana son shimfida adalci a tsakanin jama’a inji Hamidou Sidi Foddy na kungiyar kulawa da Rayuwa.
Ranar Ashura, 10 ga watan Muharram, rana ce mai muhimmanci ga duk Musulman duniya.
Wasu bangaren Musulmai su na gudanar da azumi a wannan rana domin kwatanci da Annabi (SAW). Amma ga ‘yan Shi’a, rana ce ta jimami domin kisar da aka yi wa Imam Hussaini, jikan Annabi (SAW), a Karbala a shekarar 680 Miladiya.
Your browser doesn’t support HTML5