Duk da cewar gwamnati ta haramtawa kungiyar IMN, 'yan Shi'a a Najeriya, almajiran Ibrahim El-Zakzaky sun fita sun gudanar da muzaharar ranar Ashura ta 10 ga Al-Muharram a wasu yankunan jihohin arewacin Najeriya.
Tun kafin fara muzaharar almajiran El-Zakzaky 'yan kungiyar IMN, a takaice su ka ce an kashe mu su membobi. Amma rundunar 'yan sanda ta fitar da sanarwar cewa duk wani mai son gangamin Ashura na iya fitowa kamar yadda 'yan Shi'a ke yi a sassan duniya, amma ban da 'yan kungiyar IMN da a ka haramta, kuma a ke daukar aiyukan ta na ta'addanci ne.
Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya, ya zanta da daya daga masu magana a madadin almajiran El-Zakzaky, wato Muhammad Ibrahim Gamawa bayan kammala muzaharar a karamar hukumar Lafiya ta jihar Nassarawa, domin jin tabakin sa.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar 'yan sanda ba ta fito da wata sanarwa kan wani mataki da ya kai ga asarar rayuka ba, ko kuma hukunci kan gudanar da muzaharar ta IMN.
A saurari rahoton daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum