Yan takara akalla goma sha tara ne suka fafata a zaben don neman maye gurbin Shugaba Macky Sall da rigingimun siyasa suka dabaibaye wa’adin mulkinsa na biyu.
Mutum sama da miliyan bakwai daga cikin al’ummar kasar miliyan 18 ne suka kada kuri’arsu a zaben da yunkurin jinkirta shi zuwa watan Disamban bana da Shugaba Sall yayi, ya haifar da rudanin siyasa da ba a taba ganin irinsa ba a kasar, daga bisani dai, kotun koli ta yi fatali da yunkurin tare da bayar da umarnin a gudanar da zaben ba tare da bata lokaci ba.
Ga Abubakar Bah, wannan matakin kadai abin yabawa ne da ya kasance wani sabon babi a tarihin kasar ta Senegal.
Ya ce, ‘’zan iya cewa wannan shi ne karon farko a tarihin demokradiyar Senegal da ake zaben shugaban kasa amma babu shugaba mai ci a cikin ‘yan takarar, abin da ke nufin Senegal za ta yi sabon shugaban kasa, duk da cewa shugaban kasar ya yi yunkurin ganin an dage zaben amma kuma dokar kasar bata ba shi dama ba, wanda hakan ne yasa aka iya gudanar da zaben kamar yadda aka gani’’
Kasar da ake wa kallon daya daga cikin kasashen da suka fi samun kwanciyar hankali a Afrika dai, ta gudanar da zaben ba tare da wasu shahararrun ‘yan adawa ba musanman Ousmane Sonko da hana shi shiga takarar ya haifar da rikici da asarar rayuka.
Ga Dianna Suso ta Kungiyar Hope Without Borders da ke Britaniyya ta ce, burinsu yanzu kawai su ga sauyin gwamnati. "Yawancinmu da ke kasashen waje muna son ganin sauyi, muna bukatar sabon shugaban kasar da zai ciyar da kasar gaba, dole a kawo karshen matsaloli na cin hanci da rashin aikin yi da tsadar rayuwa, muna son mu ga kasarmu Senegal ta kasance daya daga cikin kasashen duniya mafi ci gaba a duniya muna bukatar sauyi’’
Daga dai cikin ‘yan takarar da suka fafata a zaben, takarar dai tafi zafi a tsakanin Bassirou Diomaye Faye da ke samun goyon bayan Ousmane Sonko da kuma Amadou Bah wanda jam’iyyar shugaba Sall mai mulki ta BBY ta tsayar, masu sharhi dai sun soma yin hasashen irin jan aikin da ke gaban duk wanda zai lashe wannan babban zaben ganin tarin matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.
Ga wasu ‘yan Senegal da suka tsere daga kasar a sakamakon barazanar da suka ce rayuwarsu ke fuskanta a sakamakon sukar gwamnati, fatansu yanzu su koma gida doń a dama dasu. Madame Dianna ta ce "Duk yadda sakamakon ya kaya a wannan zaben dai, ya kamata mu ‘yan kasar Senegal da ke zaune a kasashen waje a sakar mana mara don mu samu mu koma gida doń muma mu taimaka wajen ayyukan bunkasa tattalin arziki, kamar noma mu daina dogaro da kayan waje a maimakon hakan mu gina matasanmu da ke fama da matsalar rashin aikin yi, zamu iya yin hakan idan mun samu damar komawa gida doń taimakawa a giną kasa da tattalin arzikin Senegal’’
A dai ranar Talata mai zuwa ake fatan sanar da sakamakon zaben, sai dai akwai yiyuwar a je zagaye na biyu muddun ba a samu dan takarar daya da ya iya lashe akalla kashi hamsin cikin dari na kuri’un da aka kada ba.
Saurari rahoton Ramatu Garba Baba:
Your browser doesn’t support HTML5