‘Yan Sandan Sakkwato Sun Kama Matashin Da Ake Zargi Da Yin Kalaman Batanci Ga Annabi

‘Yan sandan.

A Najeriya daidai lokacin da mahukunta ke gudanar da bincike akan wani matashi da ake tuhuma da yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta, gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce suna biye da batun da zimmar ganin an yi adalci.

Bayan zanga-zangar da matasa suka gudanar don neman mahukunta su dauki mataki akan matashin, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce tuni yana hannunta a cewar ASP Sanusi Abubakar kakakin rundunar a Sakkwato.

Ita kuwa gwamnatin jihar Sakkwato ta ce tana daukar matakai na tabbatar da an yi abin da ya dace kan wannan batun.

Ofishin hukumar kare hakkin bil'adama ta Najeriya da ke Sakkwato ta bakin shugaban ofishin Halilu Tambari Ahmad ya ce yana sane da batun.

A nata bangaren, kungiyar Gamayyar kungiyoyin da'awa a Najeriya cewa ta yi bai dace har yanzu ana samun masu irin wannan dabi'ar ba, a cewar shugabanta na kasa Muhammad Lawal Maidoki.

Karin bayani akan: ASP Sanusi Abubakar, Muhammad Lawal Maidoki, jihar Sakkwato, Sokoto, jihar Kano, Nigeria, da Najeriya.

Duba da cewa wannan ba shi ne karon farko na samun irin wannan matsalar ba, domin an samu irinta a jihar Kano a shekara 2008 da 2020, malaman addini ke ganin cewa da jama'a za su nemi ilimi addini da kuma aiki da shi da kuma tarbiyantar da na baya akan koyarwar addini, da ba za'a ci gaba da samun wannan masala ba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Sandan Sakkwato Sun Kama Matashin Da Ake Zargi Da Yin Kalaman Batanci Ga Annabi