‘Yan sandan Paris Sun Ba Da Hakuri Kan Hatsaniyar Ranar Wasan Karshe Na Gasar UEFA

Shugaban 'yan sandan birnin Paris, Didier Lallement (AP)

Mutane da dama ‘yan sandan Paris suka feshe da hayaki mai sa kwallo a lokacin da aka yi wata turereniya a kofar shiga filin wasan Stade de France don kallon wasan Real Madrid da Liverpool.

Rundunar ‘yan sandan birnin Paris a kasar Faransa, ta ba da hakuri kan yin amfani da hayaki mai sa kwallo akan magoya baya da iyalai a ranar wasan karshe da aka buga a gasar Champions League.

Sai dai rundunar ta kuma kare kanta har ila yau, kan daukan matakin harba fesa hayaki mai sa kwalla a lokacin da aka fara turereniya.

Mutane da dama ‘yan sandaN Paris suka feshe da hayaki mai sa kwallo a lokacin da aka yi wata turereniya a kofar shiga filin wasan Stade de France.

Real Madrid ta doke Liverpool da ci 1-0 a wasan.

Yayin wani zaman jin bahasi da majalisar Dattawan Faransa ta shirya a ranar Alhamis don duba musabbabin aukuwar lamarin, shugaban ‘yan sandan birnin na Paris, Didier Lallement, ya amsa cewa sun nuna gazawa.

“An nuna gazawa, saboda an yi ta turereniya ko kuma an ci zarafin mutane, maimakon a ce mun ba su kariya.” Lallement ya ce.

“Lallai gazawa ce, saboda kimar kasarmu ta fadi.” Lallement ya kara da cewa.

Sai dai, duk da ya amsa laifinsu, Lallement ya kare matakin da suka dauka, yana mai cewa dubban masu kallo ne suka yi cincinrundo a kofar shiga filin alhalin ba su da tikiti ko kuma suna rike da jabun tikiti.

“Hakan ya sa muka sa aka dakatar da wasan, abu muhim shi ne, ba a ji wani mummunan rauni ba kuma babu wanda ya mutu.” Lallement ya fadawa ‘ya majalisar ta Faransa.