Rahotanni daga Najeriya na cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gayyaci shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, domin ya amsa tambayoyi bayan kama wasu da ake zargin sune suka aikata fashi da makami a jihar Kwara suka ce su yaran Saraki ne.
Hedikwatar rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta nunawa manema labarai gungun wasu ‘yan jagaliyar siyasar shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Dakta Bukola Saraki, da suka tafka fashi da makami a wasu bankunan kasuwanci a garin Offa dake jihar Kwara.
Lokacin da suka gudanar da fashin ‘yan jagaliyar siyasar da a halin yanzu suka rikide suka zama rikakkun yan fashi da makami, sun bindige mutane 33 ciki har da ‘Yan Sanda 9 suka kuma yi awon gaba da bindigoginsu, daga nan suka zarce ofishin yan Sanda na garin suka ‘kara yin awon gaba da bindigogi sama da 20.
Jagoran yan fashin Ade Akinbuson, ya tabbatarwa manema labaru cewa su yan bangar siyasar shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ne Dakta Bukola Saraki, tun yana gwamna a jihar Kwara. Inda ya ce suna masa aiki irin na jagaliyar siyasa ta hanyar har hargitsa zabe a duk inda suke ganin ba za su yi Nasara ba.
Hatta motar da aka yi amfani da ita a fashin mai kirar jeep, jagoran yan fashin ya ce gwamnan kwara Abdulfatah Ahmed ne ya basu ita.
Wakilin sashin Hausa a Abuja, Hassan Maina kaina, ya tambayi jagoran yan fashin Ade ko shugaban Majalisar dattawan da Gwamnan jihar kwara suna da alaka ko masaniya dangane da wannan fashi, sai ya ce a'a, kurum dai aikin shedan ne, inda ya bayyana nadama kan wannan danyen aiki.
Hedikwatar ‘Yan Sandan ta ce jami'an ta sun bazama kudancin Najeriya, inda aka boye bindigogin jami'an ‘Yan Sandan da aka yi awon gaba dasu.
Domin karin bayani saurari tattaunar Sarfilu Hashim Gumel da Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5