Rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke Abuja hedikwatar kasar, ta gabatar da mutum 20 da ta samu nasarar cafke su wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuffuka.
Hukumomin tsaron har ila yau sun sanar da kama wasu karin mutum 11 ‘yan jami’a da ke zargin suna cikin kungiyoyin tsafi.
Nasarar hakan ta fito ne cikin bayanan da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi ya gabatar kan miyagun mutanen da ake zargi a Abuja.
A cewar Adejobi, an cafke wadanda ake zargin a wurare daban-daban a fadin kasar kuma duka sun amsa laifukkan da su suka aikata, yayin gudanar da bincike akansu.
DSP Mustapha Bello Abdulkadir ya kuma bayyana cewa an samu makamai iri-iri a hannun mutanen.
‘’Ya ce sashin binciken ‘yan sanda na FBI-IRT ya samu kwato bindigogi 27 da suka hada da guda 10 kirar AK47 da G3 guda daya da pump action guda 8, sannan akwai bindigpogin da ake kera su a Najeriya guda 3 da dai sauran manyan bindigogi da alburusai masu yawa’’.
Daga cikin wadanda aka cafke, har da wadanda suka amsa cewa su ne suka hallaka Hon. Musa Mante, dan majalisar dokokin jihar Bauchi tare da garkuwa da matansu biyu da ‘yarsa mai shekara daya, tare da wani tsohon DPO ‘yan sanda
'Yan Najeriya da ke sharhi kan sha'anin tsaro irinsu Hon. Saidu Kabiru Gombe, na da ra'ayin cewa idan ana wadatar da jami’an tsaro da kayyakin aikin da suka kamata, ba shakka kasar za ta yaki matsalolin tsaro da ke addabarta.
Har ila yau, daga cikin nasarorin da rundunar yan’sandan ta ce an samu, har da cafke wasu daga cikin gaggan ‘yan Boko Haram da suka gudu daga gidan yarin Kuje a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari, da wasu ‘yan kungiyar tsafi ta Black Axe da aka kamo su daga garin Ekpoma ta jihar Edo kuma suka amsa cewa suna wannan mugun aiki.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5