WASHINGTON, D. C. - Hukumomin ‘yan sanda a kasar Kenya sun ce sun kama Nadeem Anjarwalla, wani shugaban gudanarwa na kamfanin kudin yanar intanet (cryptocurrency) na Binance, wanda ya tsere daga Najeriya makonnin da suka gabata.
Anjarwalla dai ya tsere daga ne Najeriya biyo bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan tsarin hada-hadar kudin yanar intanet, a wani yunkuri na karfafa darajar Naira.
Yayin da hukumomin Najeriyar suka gano cewa Anjarwalla yana yankin gabashin Afirka, rahotanni da dama sun ce yanzu haka babban jami'in na Binance yana hannun 'yan sandan na Kenya.
Bisa ga rahotanni, majiyoyin gwamnati a Kenya sun tabbatar da cewa shugaban na Binance yana hannun ‘yan sandan kasar a yanzu haka.
Tun bayan da ya tsere daga Najeriya, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) da Hukumar Yaki da Manyan Laifuka ta Duniya, da Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya (NPF) da kuma Hukumar ‘Yan Sandan Kenya ke ci gaba da tattaunawa kan yadda za a tasa keyar Anjarwalla zuwa Najejeriya.
A watan Maris, hukumar EFCC ta tabbatar da shirin maido da shugaban na Binance Najeriya a cikin sanarwar hukumar ta wancan watan.