'Yan Sandan Kaduna Na Farautar Masu Tada Tarzoma A Cikin Jihar

El-Rufa'i a cikin jama'a

Gwamnatin jahar Kaduna tace mutane biyar ne aka kashe sakamakon rikicin da ya tashi a wasu sassan jihar ranar Lahadi, kuma an kama mutum uku da ake zargi da hannu kan rikicin.

Da yake jawabi ga al’umar jihar Kaduna cikin daren Litinin Gwamna Mallam Nasuru El-Rufa’i, ya ce har yanzu dokar hana yawo a garin Kaduna da kewaye na nan yadda take.

Gwanman jihar ta Kaduna ya kara da cewa wannan tashin hankalin ya samo asali daga jita-jita mara tushe da mutane suke yadawa, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane biyar a cikin tashin hankalin da ya biyo bayan fargabar da mutane suka fada a ciki sakamakon jita-jitar da ake yadawa.

Mallam El-Rufa’i yace tuni ‘yan sanda suka kama mutane uku da ake ganin suna da hannu a cikin kisar mutanen biyar, kana jami’an tsaron sun fara gudanar da bincike kuma suna bin mutanen da ake ganin sune suka haddasa wannan tashin hankali.

A cikin wannan lokaci jihar Kaduna tana fama da tashe tashen hankula a cikin birnin Kaduna da kewaye, lamarin da ya kai ga jami’an tsaron jihar daukar matakan ba-sani ba-sabo a kan duka wanda aka same shi da aikata ba daidai ba a cikin wadannan rigingimu.

Kwamishinan ‘yan-sandan jihar Kaduna CP Ahmad Abdurrahaman yace Rundunar ‘yan sanda ta dukufa wajen farautar masu hannu a cikin tada hankalin al’umma kuma za ta gurfanar da su gaban kuliya.

Rudanin daya kawo guje-guje a jahar Kaduna dai ya sa sawun kafa da na ababubuwan hawa dai sun dauke, kasuwanni da bankuna da makarantu kuma su ka rufe a garin Kaduna ranar Litinin biyo bayan dukar hana shiga da fita garin Kaduna ta saoi 24 ga gwamnati ta sa amma kuma motocin dake ketarewa zuwa wasu garuruwa sun cigaba da wuce wa bayan an tantance su.

Isah Lawal Ikara, Muryar Amurka daga Kaduna a Nageriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kaduna Crisis UPD