Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kaduna Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 55


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Jami’ai a Najeriya sun tabbatar a jiya Asabar cewa an kashe mutane hamsin da biyar a cikin wata arangama tsakanin matasan Krista da Musulmi a Arewacin Najeriya.

Tashin hankalin na ranar Alhamis ya barke ne biyo bayan wata jayayya tsakanin matasan Kristan da na Musulmi a wata kasuwa a jihar Kaduna dake tsakiyar arewacin Najeriya, a cewar mazauna yankin suna fadawa manema labarai.

A cikin wata sanarwa daga ofishin shugaban kasa, mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, yace shugaban ya yi Allah wadai da wannan tashin hankali na kasuwar Magani a Kaduna wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane hamsin da biyar.

Kwamishinan ‘yan sandan Kaduna Ahmad Abdur-Rahaman ya fada a ranar Juma’a cewa, an kama mutane 22 da suke da hannu a cikin wannan tashin hankali.

Jami’an jihar Kaduna sun fadawa kamfanin dillancin Faransa cewa an kafa dokar hana fita a kowane lokaci a yankin Kasuwar Magani inda aka yi tashin hankalin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG