Hukumar da ke kula da yi wa kasa hidima ta NYSC a Najeriya ta janye shirin tura zangon matasa na rukunin “C” zuwa Kaduna, saboda rikicin da ya barke a jihar.
Akalla mutum 55 jami’ai suka bayyana cewa sun mutu bayan barkewar rikicin wanda ke da nasaba da addini da kabilanci.
Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa hankula sun kwanta bayan da aka tura jami’an tsaro zuwa sassan jihar.
“Hukumar NYSC ta na mai sanar da dukkanin matasan rukunin “C” da aka tura zuwa jihar Kaduna wadanda za su hallara a ranar 23 ga watan Oktoba cewa an janye wannan shiri.” Inji wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Sanarwar ta kara da cewa “dukkanin matasan da aka tura zuwa jihar su zauna a gida” har sai an sassauta dokar hana fita da aka kafa.
Hukumomin sun saka dokar hana zirga-zirga har ta tsawon sa’o’i 24.
Rikicin ya samo asali ne daga yankin da ake kira Kasuwar Magani a jihar ta Kaduna wacce ta sha fama da irin wannan rikici.
Doka ce a Najeriya duk dalibin da ya kammala karatun digirinsa ko babbar difloma ya yi wa kasa hidima na tsawon shekara guda, inda akan tura su zuwa sassan kasar.
Facebook Forum