‘Yan sandan Faransa Sun Kama ‘Yar wasan PSG Ta Kungiyar Mata Aminata Diallo

Aminata Diallo

Paris Saint Germain ta ce tana bibiyar lamarin tare da shan alwashin daukan matakin da ya dace a karshe.

‘Yan sanda a Faransa sun tsare ‘yar wasan Paris Saint Germain (PSG) ta kungiyar mata Aminata Diallo bisa zargin ta da hannu a wani hari da aka kai kan wata abokiyar wasanta.

Jaridar L’Equipe ta ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba wasu mutane biyu da suka rufe fuskokinsu suka kai hari kan Kheira Hamaoui wacce ita ma take bugawa PSG wasa.

A ranar Laraba kungiyar ta PSG ta tabbatar da cewa an kama Diallo mai shekara 26.

“Mun samu tabbacin cewa ‘yan sandan yankin Versailles sun kama Aminata Diallo da wannan safiyar Laraba, a wani mataki na gudanar da bincike kan harin da aka kai wa daya daga cikin ‘yar wasanmu.” Sanarwar da PSG ta fitar ta ce.

“Paris Saint Germain tana Allah wadai da wannan hari.”

Kungiyar ta PSG ta ce tana ba ‘yan sandan Versailles hadin kai don samun bakin zaren wannan matsala.

Paris Saint Germain ta ce tana bibiyar lamarin tare da shan alwashin daukan matakin da ya dace a karshe.

Diallo, ‘yar shekara 26, ta kwashe shekara biyar tana taka leda a PSG, yayin da Hamaoui ‘yar shekara 31 ta komna kungiyar ne daga Barcelona a watan Yulin da ya gabata.