‘Yan Sandan Canada Sun Kama Matar Da Ta Yi Barazanar Kashe Wasu 'Yan Najeriya

Motar 'yan sandan Canada

Sanarwa ta kara da cewa, ana tuhumar Sonnberger, wacce 'yar kabilar Igbo ce da ke zaune a Canada da laifin furta kalamai na barazana.

‘Yan sanda a birnin Toronta na kasar Canada sun ce sun kama matar da ake zargi da yin kira da a hallaka wasu kabilun Najeriya.

A ranar 25 ga watan Agusta, Amaka Sonnberger mai shekaru 46 da ke zaune a Toronto ta wallafa wani bidiyi a shafukan sada zumunta in data yi kira da hallaka ‘Yarbawa da ‘yan yankin Benin ta hanyar saka musu guba.

“A ranar Lahadi 1 ga watan Satumba, 2024, ‘yan sandan Toronto sun kama Amaka Sonnberger.” Sanar wacce Constabel Laura Brabant ta fitar ta ce.

Sanarwa ta kara da cewa, ana tuhumar Sonnberger, wacce 'yar kabilar Igbo ce da ke zaune a Canada da laifin furta kalamai na barazana.

“Za ta gurfana a gaban kotun Ontario da ke 2201 Finch Avenue a ranar Litinin (yau,) 2 ga watan Satumba, 2024 a dakin kotu mai lamba 107.

“Ana zargin wannan al’amari na da nasaba da laifin da ya shafi nuna kiyayya.” Sanarwar ta kara da cewa.

Kalaman na Sonnberger sun janyo kakkausar suka daga cikin da wajen Najeriya.