Yan sandan Birtaniya sun saki mutane shida ba tare da tuhumarsu da wani laifi ba, kwana daya bayan kama su bisa zargin barazanar kaiwa paparoma Benedict hari.
‘Yan sandan Birtaniya sun saki mutane shida ba tare da tuhumarsu da wani laifi ba, kwana daya bayan kama su bisa zargin barazanar kashe paparoma Benedict. Hukumomi sun kama mutane biyar a wani sumame da suka kai ranar jumma’a. An kama mutum na shida sa’oi da dama bayan kama mutane biyar na farko. Jami’ai sun ce dukansu masu sharar tituna ne. jaridar Sunday Mirror ta Birtaniya ta laburta cewa, an kama mutanen ne bayanda aka ji suna wasa game da harbe paparoman da gurneti. Kafofin sadarwar kasar Birtaniya sun ce wadansu daga cikinsu ‘yan asalin kasar Algeria ne.Kakakin fafaroman yace an sanar da fadar game da kama mutanen, ya kuma ce fadar Batikan bata dauki batun a matsayin mai hatsari ba.