An yanke hukumcin daurin rai da rai a kan wani Ba-Amurke haifaffen kasar Pakistan wanda yayi yunkurin dasa bam a dandalin Times Square na birnin New York.
Jiya talata wata mai shari'a ta kotun tarayya a New York ta yanke hukumcin kan Faisal Shahzad mai shekaru 31 da haihuwa.
A watan Yuni Shahzad ya amsa laifuffuka guda 10 da aka tuhume shi da aikatawa na ta'addanci da mallakar makami. A cikin takardun da suka gabatar ma kotu a makon jiya, lauyoyi masu gabatar da kara sun ce Shahzad ya zabi wani wuri a wannan gunduma dake shake da mutane inda yake tsammanin bam din nasa zai fi yin ta'adi.
Masu gabatar da karar suka ce idan da ba a kama Shahzad ba, to yayi niyyar tayar da wani bam din bayan mako biyu a birnin na New York.
Wannan bam da ya dasa dai bai tashi ba, kuma kwanaki biyu bayan yunkurin kai harin na ranar 1 ga watan Mayu, an kama Shahzad a cikin wani jirgin saman dake dab da tashi daga New York zuwa Dubai.