Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Benedict ya ci gaba da ziyarar aiki duk da barazanar kai mashi hari da aka yi


Paparoma Benedict ya yi jawabi ga ‘yan majalisar Birtaniya ya kuma yi addu’a tare da shugaban darikar Anglican jiya jumma’a a rana ta biyu ta ziyarar farko ta ya kai kasar.

Paparoma Benedict ya yi jawabi ga ‘yan majalisar Birtaniya yayinda ya kuma yi addu’a tare da shugaban darikar Anglican jiya jumma’a a rana ta biyu a ziyarar farko da ya kai kasar. Babban Limamin darikar Katolikan ya fara gudanar da ayyukan da suka kaishi ne bayan da ‘yan sanda suka sanar da kama mutum na shida da ake kyautata zaton suna kulla makarkashiyar kaiwa paparoman hari. Paparoma Benedict shine shugaban darikar Katolika na farko da ya ziyarci fadar Lambeth, inda shugaban darikar Anglican ke zama a birnin London, tunda ikilisiyar Ingila ta balle daga Roma a shekara ta dubu da dari biyar da talatin da hudu. Paparoman da babban shugaban darikar Anglican Rowan Williams sun jagoranci sujada ta hadin guiwa a majami’ar Westminister bayan ya yi jawabi ga majalisar dokokin kasar. An bayyana wadanda suke kulla makarkashiyar kaiwa paparoman harin a matsayin masu sharar tituna. Kafofin sadarwar kasar Birtaniya sun ce wasu daga cikin mutane biyar na farko da aka kama ‘yan asalin kasar Aljeriya ne.

XS
SM
MD
LG