‘Yan sandan Birtaniya Na Bincike Kan Turereniyar Da Ta Kai Ga Mutuwar Mutum Biyu A Wasan Asake A London

Mawaki Asake (Hoto: Instagram/Asakemusic)

‘Yan sandan Birtaniya sun ce suna nazarin hotunan bidiyo tare da yin tambayoyi ga shaidu a binciken da suke yi.

‘Yan san Birtaniya sun kaddamar da bincike bayan da mutum na biyu ya mutu sanadiyyar wata turereniya da ta auku a babban dandalin wasa na O2 Brixton Academy da ke London a lokacin da mawakin Najeriya Asake yake shirin yin wasa a ranar Alhamis.

A ranar Asabar din da ta gabata, wata mata mai shekaru 33 ta rasa ranta, sannan a wannan makon wata mai gadi a gidan shakatawar mai suna Gaby Hutchinson ta mutu kamar yadda ‘yan sandan Birtaniya suka tabbatar.

Har ila yau akwai wata mata mai shekaru 21 da ke kwance a asibiti rai-kwaikwai-mutu-kwakwai

Turereniyar ta auku ne a lokacin da wasu suka yi kokarin kutsawa cikin dakin taron da karfin tuwo.

‘Yan sandan Birtaniya sun ce suna nazarin hotunan bidiyo tare da yin tambayoyi ga shaidu a binciken da suke yi.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Asake ya nuna alhininsa bisa mutuwar “Rebecca Ikumelo.”

Rebecca ita ce mutum ta farko da ta mutu bayan turereniyar.