Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a yau Litinin, tace an tura jami’an ne da nufin tabbatar da cewa al’ummar birnin sun gudanar da bukukuwan ranar samun ‘yancin kan ba tare da wata matsala ba.
Sanarwar ta kara da cewar tura jami’an zai hada dana bangaren kula da abubuwa masu fashewa da kayayyakin yaki da tarzoma da kuma wadanda zasu rika sa ido akan kai komom jama’a.
Sanarwar ta kara da cewar za’a kawar da zirga-zirgar ababen hawa daga kan hanyoyin da ake sa ran za’a samu tarurrukan jama’a ciki harda yankunan tsakiyar abuja da dandalin eagle square.
A yayin da ake gudanar da shagulgulan bikin ranar samun ‘yancin kan, ‘yan sanda sun bukaci mazauna abuja su zama masu kula, tare da kai rahoton duk wani motsi da basu yarda dashi ba ta hanyar amfani da layukan wayoyin ‘yan sanda na gaggawa.
FCT: 08032003913, 08028940883, 08061581938, 07057337653
PCB: 09022222352
CRU: 08107314192