‘Yan sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Gomman Mutane A Harin Da Boko Haram Ta Kai Yobe

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni

“An yi kone-kone, kuma har bam ma ya tashi. Wasu suna cewa mutum 80 wasu na cewa ya kai 100 mutanen da aka kashe.”

Sama da mutum 80 ‘yan Boko Haram suka kashe a garin Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Maharan sun kona gidaje tare da tayar da bama-bamai.

Bayanai sun yi nuni da cewa an yi jana'izar mutum sama da 80, a garin wanda rahotonni suke bayyana har yanzu akwai sauran gawarwaki a wasu gidaje dama gonaki.

Wani mazauin garin da ya nemi Muryar Amurka ta sakaya sunansa ya tabbatar da kashe mutanen inda ya ce akwai yiwuwar adadin ya kai 100.

“An yi kone-kone, kuma har bam ma ya tashi. Wasu suna cewa mutum 80 wasu na cewa ya kai 100 mutanen da aka kashe.”

A cewar mazaunin garin, babu jami’an tsaro a lokacin hada wannan rahoto.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Abdullahi Dungus, ya tabbatar da faruwar lamarin.

“An samu hari ne na ‘yan Boko Haram a Mafa inda suka zo don ramukon kisan ‘yan uwansu da ‘yan banga suka yi.” In ji ASP Dungus.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Mustapha:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Gomman Mutane A Harin Da Boko Haram Ta Kai Yobe.mp3