An kame mahaifiyar ‘ya‘yan Mohammed Lahouaiej Bouhlel uku ranar Juma’a. an kuma rike ta na tsawon wasu sa’o’i bayan da Bouhlel ya tuko katuwar mota da tafiyar tsawon kilomita 90 zuwa cikin birnin Nice, inda ya kashe mutane 84.
Lauyan matar ya fadawa gidan talabijin na Faransa cewa, bata da wata alaka da shi, bayan da ta kore shi daga gidanta lokacin da ya doketa.
Jami’ai sunyi imanin cewa Bouhlel ya aika da sakon karta kwana na wayar hannu minti 18 kafin ya kai harin, yana cewa “ka kawo ‘karin makamai, ka kawo guda biyar zuwa C,” har yanzu dai ba a san mai yake nufi da harafin C ba.
Cikin mutane shida dake hannun hukuma akwai mutumin da ake tunanin shi ne aka aikawa sakon karta kwanan, da kuma wata mace, baki daya dai an kama su ranar Lahadi.