Mafi yawancin Amurkawa suna kara samun fargabar yanayin yakin neman zaben da ke gudana a Amurka na neman shugabancin mashahuriyar kasar. Jaridar Washington Post ta aiwatar da wani sabon inciken hada alkaluma.
Wanda wannan binciken jin ra’ayin ya nuna cewa, kaso 63 na Amurkawa na tunanin cewa yakin neman zaben yana kara muni kuma baya tafiya akan hanya daidai. Kididdigar da ta haura akan ta baya yawansu bai wuce kashi 48 ba.
Kashi 72 na Bakaken fatar Amurka na da fargabar akwai nuna bambancin launin fata a yakin neman zaben. Inda suka bada misali da kashen bakaken fata 2 na kwanan nan da ‘yan sanda suka yi, shima wani bakar fatar ya bindige wasu ‘yan sandan har lahira a Dallas.
Wannan wariyar launin fatar na iya zama wata dama ga cin zaben Hillary Clinton, inda kididdigar ta nuna kashi 58 na da yakinin zata iya shawo kan matsalar wariyar jinsin. Duk da cewa Trump yace shi baya cikin masu nuna wariyar jinsi ko launin fata.