'Yan Sanda Sun Kubutar Da Turawan Amurka Da Canada Da Aka Sace

Wasu 'yan sanda Najeriya yayin da suke bakin aiki

'Yan sandan Najeriya sun kubutar da wasu turawan Amurka da Canada da aka yi garkuwa da su tare da cafke biyu daga cikin masu satar mutanen da safiyar yau Asabar.

Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan sandan kasar sun yi nasarar kubutar da wasu turawa hudu da aka yi garkuwa da su a kasar farkon makon nan.

Turawan sun hada da mutane biyu ‘yan kasar Canada da kuma wasu biyu Amurkawa, wadanda aka yi garkuwa da su a ranar Talatar da ta gabata.

Wata majiya a ofishin ‘yan sanda Najeriya da ta nemi kada a bayyana sunanta, ta fadawa wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina cewa, an mika wadanda aka kubutar din ga ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja.

Mutanen sun hada da Vangees dan kasar Canada da John Kirlin ba’amurke da Rachel Kelley ‘yar kasar Canada da kuma Dean Slocum ba’amurke.

Rundunar ‘yan sanda Najeriya ta ce an kuma yi nasarar cafke biyu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da turawan.

Babu dai wani bayani da ya nuna cewa an yi yunkurin biyan kudin fansa domin kubutar da su.

A ranar Talatar da ta gabata ne aka sace turawan yayin da suke tafiya akan hanyar Kaduna da Abuja, wacce tunga ce ta masu garkuwa da mutane domin neman kudaden fansa.

Saurari rahoton da Hassan Maina Kaina ya aiko mana:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Sanda Sun Kubutar Da Turawan Amurka Da Canada Da Aka Sace - 1'06"