Jami’an ‘yan sanda sun kama mutane 130 da suke zargi da laifuffukan intanet da yin kutsen na’ura.
Wadanda ake tuhumar sun hada da ‘yan Najeriya 17 da bakin haure 113, a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi a jiya Lahadi.
A sanarwar da ya fitar Adejobi yace, ayyukan mutanen na barazana ga tsaron Najeriya.
An gudanar da wannan kame ne sakamakon samamen da aka kai kan wani gini a unguwar Jahi, dake birnin Abuja, inda rahotanni suka ce mutanen na amfani da komfutoci da na’urorin zamani wajen aikata laifuffuka,” a cewarsa.
“Samamen wanda ya gudana karkashin jagorancin mukaddashin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da shiya ta 7, ta birnin abuja, aig benneth igweh, a ranar asabar, 3 ga watan nuwamban da muke ciki, ya kunshi jami’ai daga shiya ta 7 ta rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Abuja dana rundunar yaki da laifuffukan intanet ta Najeriya (npf-nccc).”
Ya kara da cewar har yanzu rundunar na gudanar da bincike akan lamarin, inda yace ana tantance kayayyakin da kwato daga mutanen ta hanyar binciken kimiya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan yace za’a gurfanar da mutanen a kotu da zarar an kammala binciken.