Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Tsohon Babban Jojin Najeriya Onnoghen Daga Zargin Bada Bayanan Kadarorin Bogi

Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Walter Onnoghen,
Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Walter Onnoghen,

Kotun daukaka karar ta yi watsi da tuhumar da ake yiwa Onnoghen ne sakamakon samun maslahar da aka yi a kan batutuwan da suka kai ga shari’a dama tuhumar tasa.

Kotun daukaka kara dake Abuja ta sallami tare da wanke tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Walter Onnoghen, daga tuhumar da kotun da’ar ma’aikata ke masa ta bada bayanan bogi a kan kadarorin da ya mallaka.

Kotun daukaka karar ta yi watsi da tuhumar da ake yiwa Onnoghen ne sakamakon samun maslahar da aka yi a kan batutuwan da suka kai ga shari’a dama tuhumar tasa.

A ranar 25 ga watan Janairun 2019 ana kimanin kwanaki 29 gabanin zaben shugaban kasa, tsohon shaugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya dakatar da Onnoghen daga kan mukamin babban jojin Najeriya tare da rantsar da alkalin dake biye da shi a girman mukami a kotun kolin, Mai Shari’a Tanko Muhammad, ya jagoranci bangaren shari’ar kasar.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Abba Muhammad, ya amince da sharuddan sulhu tsakanin gwamnatin Najeriya da Onnoghen.

Ya kuma ba da umarnin budewa tsohon babban jojin Najeriya da asusun ajiyar bankinsa 4 da aka rufe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG